Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF ta dakatar da kocin ‘yan wasan Najeriya wato Super Eagles Salisu Yusuf na shekara daya.
Hukumar NFF ta dauki wannan mataki ne bayan kwamitin da ta kafa karkashin tsohon shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya bincika tare da samunsa da laifin karbar cin hanci.
A kwanakin baya wani faifan bidiyo ya bayyana a shafukan sadarwa, inda aka nuna wasu mutane suna ba Salisu Yusuf kudi.
Hakanan kuma hukumar ta bukaci kocin ya biya tarar $5,000 nan da wata uku.