✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage kulob din Nocerina da ’yan kwallo shida a Italiya

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar kwallon kafa ta Italiya (FA) ta bayar da sanarwar dage kulob din Nocerina da yin wasa a matakin rukuni na…

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar kwallon kafa ta Italiya (FA) ta bayar da sanarwar dage kulob din Nocerina da yin wasa a matakin rukuni na uku na gasar rukunin kasar saboda abin kunyar da ya aikata.
A wasan da kulob din ya yi a karshen makon jiya ne aka samu matsala bayan shida daga cikin ’yan kwallonsa suka rika yanke jiki suna faduwa a tsakanin mintuna 20 saboda raunukan da suka ji.&nbsp Hakan ta sa aka fitar da su fili kuma biyar ne kacal daga cikin 11 na ’yan kwallon suka rage kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Daga nan ne alkalin wasa ya dage wasan kuma ya aika rahotonsa ga Hukumar shirya kwallon Italiya.
Nan take Hukumar ta bayar da sanarwar hukunta kulob din ta hanyar mayar da shi matakin rukunin ’yan dagaji daga rukuni na uku saboda wannan abin kunya.&nbsp Sannan an ci tararsa Dala dubu 13 da 700 kwatankwacin Naira miliyan biyu da dubu dari uku.
Su kuwa daukacin ’yan kwallon da al’amarin ya rutsa da su an dage su daga yin kwallo har na tsawon shekara daya tare da jami’ansu yayin da aka wanke sauran ’yan kwallo shida da al’amarin bai shafa&nbsp ba.
Shi kuma shugaban kulob din Luigi Benebento an dage shi ne&nbsp tsawon shekara uku da rabi tare da Daraktansa Luigi Pabarese da kuma Likitan kulob din mai suna Giobanni Rosati.