✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage gasar kwallon kwandon makarantun sakandare a Legas saboda Ebola

Kamfani Nestle wanda ke yin Milo ya dage gasar kwallon kwandon makaratun sakandare karo na 16 a Jihar Legas saboda cutar Ebola.Da farko an sanya…

Kamfani Nestle wanda ke yin Milo ya dage gasar kwallon kwandon makaratun sakandare karo na 16 a Jihar Legas saboda cutar Ebola.
Da farko an sanya za a fara gudanar da gasar a ranar Talata ne, amma saboda bullar cutar Ebola a jihar sai aka mayar 16 ga wannan watan.
Tuni makarantu 12 da za su fafata a gasar suka iso Legas.
Mai magana da yawun kamfanin Nestle Dokta Samuel Adenekan ne ya sanar da batun dage gasar.
“Saboda al’amarin da ya shafi kiwon lafiya kamfanin Nestle Nigeria Limited yake sanar da dage gasar kwallon kwandon makaratun sakandare karo na 16 da aka shirya gudanar da ita a filin wasa na kasa daga 12 zuwa 16 ga Agusta, 2014. Kodayake za a sanar da tabbatacciyar ranar da za a fara gasar bayan an ga yanayin cutar Ebola.” Inji shi.
Makarantun 12 ne za su fafata a wannan gasar inda daga Arewa akwai Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Numan, da General Murtala College, Yola duka a Jihar Adamawa da Gobernment Secondary School, Gboko, Jihar Benuwai da Dutse Model International da Kwalejin Gwamnatin ’Yan Mata duk a Jihar Jigawa.