✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya sassauta dokar hana fita a Kano

An sassauta dokar ce daga karfe 12 na rana zuwa karfe na yamma a ranar Juma'a kadai.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sassauta dokar hana fita domin a samu damar gudanar da Sallar Juma’a.

Gwamantin jihar ta sassauta dokar ce daga karfe 12 na rana zuwa karfe 5 na yamma a ranar Juma’a kadai.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Haruna Isah Dederi, ya roki Allah Ya zaunar da jihar lafiya.

Gwamnatin Kano ta sanya dokar ce bayan zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar ta rikiɗe ta koma tarzoma da sace-sace.