Yanzu haka jami’an tsaro sun bazama a kasar Kenya don zakulo wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani mai goyon bayan kulob din Liberpool da ke Ingila mai suna Anthony Mutueitha ta hanyar daba masa wuka jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin kulob din Liberpool da na Arsenal a ranar Asabar da ta wuce.
A wasan, kulob din Liberpool ne ya yi kaca-kaca da na Arsenal da ci 5-1 a gasar rukunin Premier na Ingila
Wani da al’amarin ya faru a kan idonsa wanda ba a ambaci sunansa ba ya ce a gidan shan barasa na Meru da ke Kenya ne al’amarin ya faru. Ya ce an soka wa matashin wuka ne a lokacin da yake murnar kulob dinsa Liberppol ya samu nasara a kan na Arsenal da ci 5-1. Yana cikin murnar ne wani da ba a tantance kowane ne ba ya lallaba ta bayansa ya burma masa wuka ta baya kuma kafin ka ce kwabo ya zube kasa yana neman agaji. Nan da nan wadanda ke wurin suka ranta cikin na kare tare kuma aka rasa wanda ya aikata hakan. Daga baya aka garzaya da shi asibiti amma kafin ka ce kwabo ya sheka barzahu.
Matasan Kenya na da sha’awra kallon wasan kwallon gasar Premier ta Ingila don haka a duk lokacin da wasa ke gudana sukan yi cincirindo a gidajen kallo da kuma wuraren shakatawa don kashe kwarkatar idanu.
Al’amarin kisan kai a lokacin da ake kallon kwallo ba sabon abu ba ne a Kenya don an sha samun faruwar irin haka a shekarun baya.
A shekarar bara wani mai goyon bayan kulob din Manchester United ya hallaka kansa jim kadan bayan kulob din Newcastle ya doke na United a gasar ta Premier.
Haka kuma a shekarar 2009, an samu labarin yadda wani dan Arsenal ya rataye kansa bayan kulob din Manchester United ya doke na Arsenal.
Ya zuwa wannan lokaci jami’an ’yan sanda ba su samu nasarar kama wanda ya aikata kisan ba, amma sun tabbatar da cigaba da gudanar da bincike.
An daba wa wani mai goyon bayan Liberpool wuka a Kenya
Yanzu haka jami’an tsaro sun bazama a kasar Kenya don zakulo wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani mai goyon bayan kulob din Liberpool da ke…