Likitoci sun cire wuka mai tsatsa a cikin kokon kan wani mutum bayan ya shafe shekara 26 yana fama da ita.
Wukar mai tsawon inci 4 ta kasance a cikin kansa tun lokacin da aka buga masa ita a lokacin wata hayaniya a 1994.
Mutumin da ake kiransa da suna Mista Duorijie, dan shekara 76, ya shaida wa likitoci yadda yake fama da ciyon kai mai tsanani a 2012.
Sai dai tun da fari likitoci sun ce ba za a cire wukar ba saboda za ta yi sanadiyyar rasa ransa sakamakon cirewar.
Daga karshe an samu nasarar cire wukar a asibitin Shandong Kianfoshan da ke kasar China, wanda aka bayyana al’amarin da ‘baiwa’.
Hotunan kokon kan Mista Duorijie, wadanda aka dauka a yankin Jinan babban birnin Shandong, sun bayyana wukar wacce take ta yankan lemo ce a keyar mutumin.
Duorijie, wanda ya fito daga kauyen Haiyan Arewa maso Yammacin China, an yi masa aiki har sau biyu a cikin watan Afirilu, inda ya shafe tafiya ta kimanin mil dubu 1,860 domin zuwa inda za a yi masa wannan tiyata. Sakamakon yankin da ya fito babu isassun kayan aiki.
Dakta Zhang Shudiang, yana daya daga cikin wadanda suka yi wa Duorijie, aiki ya ce “a lokacin da muka hadu da shi muna cikin wata tawaga ta likitoci da aka tura kinghai.
“Mun lura da matsalar Duorijie, likitoci suna rubuta masa maganin rage radadin zafin ciwo ne kawai, amma yanayin ciwon da yake fama da shi ya tsananta matuka, wanda ba za a jure masa ba.
“Sakamakon rashin isassun kayan aiki da ake fama da shi a yankunan karkara.
“Sai muka yanke shawarar kawo shi Shandong, don yi masa magani”, inji shi.
Daga cikin irin matsalar da Duorijie yake fama da ita ta hada da matsalar gani ta bangaren dama sannan rabin jikinsa yana fuskantar shanyewa.
Kwararun likitoci na asibitin Shandong kianfoshan da suka hada da babban likitan kunne da hanci da baki suna daga cikin wadanda suka halarci tiyatar.
Hoton kokon kan mutumin ya nuna yadda wukar ta makale a cikin kan nasa wanda ta nufi gurbin idonsa ta baya.
Babban likitan tiyata a asibitin Mista Liu Guangcun, ya amince cewa babu wata hanya ta magance wannann matsala face a cire masa wannan wuka wacce tsawonta ya kai inci 4 fadinta kuma inci 1.2, domin ya fita daga cikin kangin da yake ciki.
Dakta Zhang ya ce “tiyatar ta shafe tsawon sa’a biyu kafin a cire masa wukar daga cikin kansa, wacce ta yi tsatsa.
Ranar 8 watan Afirilu, aka shiga tiyata ta biyu inda aka samu nasarar wanke masa wurin da ya yi rauni, yana samun sauki sannan yana tafiya da kafarsa.
Tsananin ciwon kan da yake fama da shi yanzu babu, sannan ganinsa ya dawo.
Duorijie ya ce “a da ba zan iya dariya ko gatsine ba ko kuma tari.
“A yanzu likitoci sun ceto rayuwata, inda zan sake rayuwa a karo na biyu tun bayan shekara 20 da suka gabata”, inji shi.