✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci tarar Giwa FC bayan an dage ’yan kwallonta biyu

Hukumar shirya gasar rukuni-rukuni ta kasa (NPFL) ta bayar da sanarwar dage ’yan kwallo biyu na kulob din FC Giwa da ke garin Jos. ’Yan…

Hukumar shirya gasar rukuni-rukuni ta kasa (NPFL) ta bayar da sanarwar dage ’yan kwallo biyu na kulob din FC Giwa da ke garin Jos. ’Yan kwallon biyu da hukumar ta dage su ne Amos Gyang da kuma Nojeem Raji

Hukumar ta ce ta dage ’yan kwallon ne saboda rashin da’a da suka nuna a wasan karshe da kulob din ya yi da na Nasarawa United a gasar rukuni-rukuni na kasa da aka kammala a ranar Lahadin da ta wuce.
An dage Amos Gyang ne bayan an same da laifin cin zarafin wani matashi mai dauko kwallo idan ta fita daga fili (ball boy) inda nan take alkalin wasa ya ba shi katin kora (red card) amma dan kwallon ya ki barin filin.
Shi kuwa Nojeem Raji an same shi da laifi ne bayan ya zagi alkalin wasan jim kadan bayan ya ba takwaransa Gyang jan kati, inda shi ma nan take alkalin wasan ya ba shi nasa jan katin, amma shi ma ya ki barin filin.
An samu ’yan kwallon da wannan laifi ne bayan hukumar shirya wasannin ta kafa wani kwamitin bincike. Sannan a daidai minti 34 ne kulob din Giwa ya dakatar da wasan, a lokacin da Nasarawa United ke kan gaba da ci 2-0.
Hukumar NPFL ta ce ta zaftare maki uku da kwallaye uku ga Giwa FC bayan tarar Naira miliyan uku da ta kakaba wa kulob din.
Su dai ’yan kwallo biyun da aka dakatar da kuma hukuncin da aka yanke wa Giwa FC suna da damar daukaka kara idan har ba su gamsu ba a tsakanin awanni 48 da yanke hukuncin.