✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci tarar dan majalisa saboda ya yi fitsari cikin mutane

Kotu ta ci tarar wani dan majalisa a kasar  Uganda saboda ya yi fitsari a cikin mutane. Kotun da ke zama a birnin Tarayyar kasar…

Kotu ta ci tarar wani dan majalisa a kasar  Uganda saboda ya yi fitsari a cikin mutane. Kotun da ke zama a birnin Tarayyar kasar ta sa Abraham Abiriga ya biya 40,000 na kudin Uganda wanda yake dai dai da Dalar Amurka 10 saboda laifin da ya yi ya janyo cece-kuce a cikin jama’a.  Dan majalisar kuma tuni ya biya tarar.

An dauki hoton Abiriga a karshen watan Satumba yana fitsari a kusa da kofar ma’aikatar kudade, inda hoton daya jawo cece kuce a kafafen yada labarai wanda ya jawo aka kama shi aka maka shi a kotu.

New vision portal su ka yi rahoton cewa mai kara ya tabbatar da cewa Abiriga ya karya dokar birnin Kampala ta shekarar 2016.

A lokacin afkuwar abin, ya kare kansa da cewa fitsarin ne ya matseshi sosai shi ya sa ya yi wannan aika aika.