Wata Babbar Kotu a Jihar Delta ta ci dan takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar SDP, Kenneth Gbagi tarar Naira miliyan daya kan zargin take ’yancin wani mai suna Victor Ephraim.
Kotun da ke zamanta a Warri karkashin jagorancin Mai Shari’a Vera Agbodje, ta ci tarar dan takarar ne a Litinin.
Lauyan mai shigar da kara, Kunle Edun, ya shigar da kara mai lamba EHC/FHR/80/2020 a madadin wanda yake karewa a kan Gbagi da wani otel dinsa.
Mai kare kansa wanda kuma tsohon ma’aikacin otel din Gbagi ne, ya yi zargin cewa tsakanin 17 da 18 ga Satumban 2020, Gbagi ya sa jami’an da ke gadinsa suka yi masa tsirara sannan jefa shi a bayan motarsa ya tafi da shi har kauyensu.
Ephraim ya shaida wa kotun cewa, bayan tsare shi ta haramtacciyar hanya, an kuma gana masa bakar azaba da ci masa mutunci tare da wasu mata ma’aikatan otel din su uku.
Ya ce dan takarar ya sa an ci musu mutunci ne kan zargin kin mika wasu kudaden otel din da aka samu wanda hakan ya sa ya karbe katin ATM dinsu sannan ya kwashe kwadadensu daga asusun ajiyarsu zuwa asusun otel din.
Bayan jin bayanin kowane bangare, Alkali Agbodje ya ce dukkan bayanan da Gbagi ya gabatar wa kotun karya ce, kotun ba ta gamnsu da su ba.
Haka nan, ya ce Gbagi ya dauki doka a hannunsa na gana wa tsohon ma’aikacinsa azaba, don haka ya yanke hukuncin tarar Naira miliyan daya a kan dan takarar da otel dinsa ga Ephraim.
Sai dai, Gbagi ya ce hukuncin kotun wani shiri ne na Gwamnatin Ifeanyi Okowa na neman dakile shi, wanda a cewarsa hakar gwamnatin ba za ta cim ma ruwa ba.