Rahotanni daga Jihar Kano sun nuna cewa an ceto wata yarinya ’yar shekara 15 da iyayenta suka rufe tsawon shekara 10 a daure.
A Litinin din ta gabata ce rundunar ’yan sanda a jihar ta ceto yarinyar mai suna Aisha Jibrin wacce aka kulle a daki tun tana ’yar shekara biyar.
- Sabuwar gasar ‘Super League’ ta janyo rabuwar kai a Turai
- Babu kudirin kara farashin man fetur a watan Mayu — NNPC
Sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta nuna cewa, sun samu rahoton yarinyar da misalin karfe 11.00 na safe, inda nan take Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Habu Ahmed Sani ya bayar da umarnin a gaggauta ceto.
Aminiya ta ruwaito cewa, an ceto yarinyar ce cikin wani mawuyacin hali na tsananin yunwa da bukatar kula da lafiyarta saboda irin yanayin da suka samu wurin da aka kulle ta a unguwar Derawa da ke Karamar Hukumar Fagge.
A yanzu haka dai ana duba lafiyar yarinyar a asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kanon inda aka garzaya da ita domin ba ta kulawar da ta dace.
Tuni ’yan sandan suka cafke mahaifiyarta mai shekara 35, Rabi Muhammad, yayin da shi kuma mahaifinta, Muhammad Jibrin ya bazama.
A bara ce ’yan sanda a Kano suka ceto wani matashi da mahaifinsa ya turke a daki tsawon shekara 15 da niyyar yi masa kisan mummuke bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Kazalika, irin haka ta faru cikin watan Agustan bara a Kano, inda ’yan sanda suka ceto wani matashi da mahaifinsa ya kulle a daki tsawon shekara uku ba tare da ba shi damar fita ba.
Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da ’yan sanda suka gurfanar da mahaifin wani yaro da aka ceto a Birnin Kebbi, wanda aka zargi matan ubansa da dauke shi a turken dabbobi tsawon shekara biyu.