✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto yaran mata 5 daga karuwanci a Edo

Hukumar tsaro ta Sibil Difens, a Litinin da ta gabata ta ceto wasu yaran mata 5 daga wata maboya, inda ake koya wa mata karuwanci…

Hukumar tsaro ta Sibil Difens, a Litinin da ta gabata ta ceto wasu yaran mata 5 daga wata maboya, inda ake koya wa mata karuwanci a Jihar Edo.

A cikin yaran matan, har da wata mata da ta ayyana cewa shekararta 20 a duniya. An ceto su ne a yayin da jami’an hukumar suka gudanar da aiki na musamman a yankin Uselu N’ahor na karamar Hukumar Uhunmwode, Jihar Edo. Kwamandan hukumar a jihar, Makinde Ayinla ya ce yaran matan da aka ceto an kawo su ne daga Arewacin Najeriya.

Wasu daga cikin yaran matan da aka ceto, sun bayyana wa wakilinmu cewa an kawo su ne daga Jihar Biniwai. Sun ce iyayensu na da masaniyar cewa za a kawo su nan Jihar Edo ne. Sun kara da cewa wata mata ce da ake kira da lakanin Manaja ta dauko su, bisa alkawarin cewa za su yi aiki ne a otel din sayar da giya. 

Yaran sun ce ita matar, wacce a yanzu haka ta tsere, sai da ta amshi Naira dubu 30 daga kowace yarinya, kafin ta bar su su fara karuwanci na kashin kansu. “Kullum muna biyan ta Naira 500 kudin daki, inda mu kuma a kullum muke samun Naira dubu 3 zuwa dubu hudu a harkar karuwanci,” inji yaran matan.