✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto ‘yar shekara 4 daga masu garkuwa da kame ‘yan Boko Haram 3 da wasu 84 a Kano

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano, ta yi nasarar kubutar da yarinya ‘yar shekaru 4 daga hannun wasu mutum 3 ‘yan asalin jihar Kaduna da suka…

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano, ta yi nasarar kubutar da yarinya ‘yar shekaru 4 daga hannun wasu mutum 3 ‘yan asalin jihar Kaduna da suka yi garkuwa da ita.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Iliyasu, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar 4 ga watan nan ne wasu jami’an rundunar na musamman suka kame wani mutum mai suna Ibrahim Musa, wanda ya bada bayanan da aka kai ga kame karin wasu mata biyu dukannin su ‘yan jihar Kaduna aka kubutar da yarinyar mai suna Khadija Ridwan mai shekaru 4 ‘yar jihar Kano.

Sashin makamai da na’urorin da batagarin ke amfani dasu

Ya ce, Hukumar ta kuma kame wasu ‘yan kungiyar Boko Haram 3 “An kama daya ne a wani gidan baki a unguwar Sabon Gari yayin da aka kame na biyun a cikin birnin Kano a wata maboyar bata gari, kuma a binciken da muka yi masu dukkanin su sun amsa cewa su ‘yan kungiyar Boka Haram ne da ke kokarin hada karfi su kai hari”.

Hukumar ‘yan sandan ta Kano ta kuma kama mutum 87 da ake zargi da laifukan da suka shafi fashi da makami garkuwa da mutane, sha ko hadadar miyagun kwayoyi da sauran su inda ta kame tarin makamai da suka hadar da bindigogi harsashai, adduna, barandami, gariyo da makamantan su.

Wadanda ake zargi da laifi da Hukumar ta kame

A cikin makwanni biyar da fara jan ragamar Hukumar ‘yan sandan jihar a matsayin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Iliyasu, rundunar ta yi nasarar wadanda ake zargi da laifin guda 360, ya ce rundunar zata ci gaba da farautar masu laifi tare da kakkabe su daga birnin na Kano.