Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da ceto wasu ‘yan mata 26 daga hannun masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Tuni aka kammala shirye-shiryen sada ‘yan matan da iyayensu bayan kwararrun ma’aikatan lafiya sun tabbatar da koshin lafiyarsu da kuma cewa ba sa fama da wani firgici sakamakon garkuwar da aka yi da su.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Zamfara
- An hallaka mutum 5 a Katsina bisa zargin garkuwa da mutane
Gwamnan jihar, Bello Matawalle shine ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.
Ya ce an sami nasarar ceto ‘yan matan ne ranar shida ga watan Nuwamban 2020 wadanda galibinsu an sace su ne daga jihar Katsina sakamakon jajircewar gwamnatinsa.
Matawalle ya ce, “Za mu ci gaba da amfani da hanyoyin karfi da na maslaha wajen magance matsalar ‘yan bindigan da ta addabi jihohinmu na Arewa Maso Yamma, duk kuwa da matsin tattalin arzikin da muka gada a jihar mu.”
Sai dai Gwamna Matawalle ya nemi tallafin Gwamnatin Tarayya wajen yakar ‘yan ta’addan da suka addabi yankin ta hanyar samar musu da isassun kudade.
Matawalle ya ce sun sami nasarar kubutar da ‘yan matan ne a irin manufofinsu na rashin yin amfanai da karfin tuwo, wanda hakan ne ma yasa aka sako su ba tare da wani sharadi ba.
Rahotanni dai sun nuna ‘yan matan sun shafe kusan mako daya a hannun masu garkuwar, kuma tuni suka kama hanyar komawa ga iyayensu bayan an mika su ga gwamnatin jihar Katsina a hukumance.
Jihohin Zamfara da Katsina dai dake yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta ‘yan bindiga da ta masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta fi kamari.