Hukumar NAPTIP Mai Yaki da Masu Safarar Mutane a Najeriya, ta sanar da ceto wasu mutum 52 a Jihohin Kano da Jigawa da Katsina da ke Arewacin kasar, wadanda aka yi yunkurin safararsu.
Shugaban Hukumar reshen Jihar Kano, Abdullahi Babale wanda ya inganta rahoton, ya ce za su tabbatar sun tsananta sanya idanun lura domin ci gaba da kama masu safarar mutane a Arewacin kasar.
- Murnar Sallah: Ganduje ya ’yantar da fursunoni 123 a Kano
- Yadda sauran masu sallar Tahajjud 10 da aka sace a Katsina suka kubuta
Sanarwar da Babale ya fitar yayin zanta wa da manema labarai na Gidan Talabijin din kasa na NTA, ta ce an kama mutum hudu da ke zargi da aikata laifin a Jihohin Imo, Delta, Edo, Ondo da kuma Ogun.
Ya ce an kama su ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Libiya sannan su karasa Turai inda za su ci kasuwarsu a can.a
Daga cikin mutum 52 wadanda aka ceto, akwai mata 48 da maza hudu ’yan tsakanin shekara 16 zuwa 34.
Yayin zantawarta da manema labarai a birnin Dabo, Shugabar Hukumar NAPTIP ta kasa, Julie Okah-Donlie, ta ce masu fataucin mutane basu da wurin buya a kasar nan.