✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 5 daga hannun masu garkuwa da mutane

’Yan sanda sun kubutar da matafiya biyar da ’yan bindiga suka yi gakruwa da su a hanyar Benin zuwa Auchi a Jihar Edo. Masu garkuwar…

’Yan sanda sun kubutar da matafiya biyar da ’yan bindiga suka yi gakruwa da su a hanyar Benin zuwa Auchi a Jihar Edo.

Masu garkuwar sun tare wata mota kirar Toyota Siena, suka yi awon gaba da mutum takwas da ke cikin motar kafin daga baya jami’an tsaron su bi sawunsu.

Ganin jami’an tsaron ya sa suka tsere suka bar biyar daga cikin matafiyan, amma suka tafi da sauran mutum ukun.

’Yan sanda sun kuma cika hannu da ’yan fashin mota uku a lokacin da suke kokarin yin awon gaba da motocin da suka sace.

Dubun ’yan fashin ta cika ne bayan sun kwace wasu motoci biyu da bakin bindiga a garin Ekpoma na jihar.

Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, kongtons Bello, ya ce an kama ’yan fashin ne suna kokarin barin garin, aka kuma kwace motocin.

A cewarsa, rundunar ’yan sandan jihar za ta ci gaba da yin duk abin da ya dace domin tabbatar da tsar a jihar.