Jami’an tsaro sun ceto matasa 47 da ke tsare a wani gidan kangararru ba bisa ka’ida ba a Kano.
A ranar Alhamis ’yan sanda suka ceto matansan a gidan wani a unguwar ’Yar Akwa a Karamar Hukuamr Tarauni ta jihar.
- Mako biyar da sallamar Nanono, Buhari bai nada mistan naoma ba
- An yanke wa Faisal, dan Abdulrasheed Maina daurin shekara 24
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce wadanda aka ceto din shekarunsu 12 ne zuwa 30, dukkaninsu maza.
Kakakin Rundunar, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan an ceto su, an kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin duba laifyarsu.
Ya ce, “A galabaice suke, jikinsu duk rauni saboda tsabar duka da azabtarwa da ake musu a cibiyar.”
A cewarsa, mutum biyu da ke kula da cibiyar sun shiga hannu, za a gurafanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Masu cibiyar sun tabbatar cewa sun kusa shekara guda suna tafiyar da ita duk da haramcin da Gwamnatin Jihar Kano ta sanya.
Sai dai kuma sun yi roko da cewa a yi musu afuwa.
A watan Nuwamban 2019 ne Gwamnatin Jihar Kano ta haramta gudanar da ciboyin horon kangararrun yara ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.