✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto leburori 25 da bene mai hawa 7 ya rushe a kansu a Legas

An ceto leburori 25 da suka makale a cikin baraguzan wani bene mai hawa bakwai da suke aikin ginawa da ya rushe da su a…

An ceto leburori 25 da suka makale a cikin baraguzai bayan wani bene mai hawa bakwai da suke aikin ginawa ya rushe da su a ciki a Jihar Legas.

Gwamnatin Jihar Legas ce ta sanar da hakan bayan faruwar iftila’in a ginin da ya rushe a yayin da ake tsaka da aikin ginin sa a yankin Banana Island da ke jihar.

Kwamishinan Yada Labaran jihar, Gbenga Omotoshi, wanda ya sanar da haka, ya ce, mutum 16 da suka samu raunuka sosai an kwantar da su a asibitoci, ragowar taran kuma da ba suka samu kananan raunuka ko kukkujewa an riga an sallame su.

Sanar da ya fitar ta ce ana ci gaba da aikin ceto, kuma gwamnatin jihar ta fara gudanar da bincike kan rushewar da benen mai hawa bakwai da ya auku a ranar Laraba.

Ya kuma bayyana cewa. Gwamna Babajide Sanwolu jihar ta kuma ba da umarnin dakatar da duk aikin gine-ginen da ake yi a yankin domin tantance ingancinsu.