An ceto leburori 25 da suka makale a cikin baraguzai bayan wani bene mai hawa bakwai da suke aikin ginawa ya rushe da su a ciki a Jihar Legas.
Gwamnatin Jihar Legas ce ta sanar da hakan bayan faruwar iftila’in a ginin da ya rushe a yayin da ake tsaka da aikin ginin sa a yankin Banana Island da ke jihar.
- Shekara 9 da sace Daliban Chibok, har yanzu 98 na hannun Boko Haram
- Zaben Gwamnan Kogi: Yahaya Bello ya ki goyon bayan mataimakinsa
Kwamishinan Yada Labaran jihar, Gbenga Omotoshi, wanda ya sanar da haka, ya ce, mutum 16 da suka samu raunuka sosai an kwantar da su a asibitoci, ragowar taran kuma da ba suka samu kananan raunuka ko kukkujewa an riga an sallame su.
Sanar da ya fitar ta ce ana ci gaba da aikin ceto, kuma gwamnatin jihar ta fara gudanar da bincike kan rushewar da benen mai hawa bakwai da ya auku a ranar Laraba.
Ya kuma bayyana cewa. Gwamna Babajide Sanwolu jihar ta kuma ba da umarnin dakatar da duk aikin gine-ginen da ake yi a yankin domin tantance ingancinsu.