Dakarun Rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar kubutar da wasu direbobin manyan motoci hudu da wasu da ake zargin ’yan kungiyar ISWAP ne suka yi garkuwa da su a Jihar Borno.
An dai sace direbobin ne a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu a wani daji da ke kusa da kauyen Ngwom na Karamar Hukumar Mafa.
Mafa na da tazarar kilomita 50 daga gabas da Maiduguri, babban birnin Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru yayin da direbobin suka kai wasu masu yankan itace daji, inda a nan ne ‘yan ta’adda dauke da makamai suka tare su.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun tare direbobin ne da sunan cewa suna bukatar aikinsu domin kai wasu mambobinsu wani kauye da ke kusa.
Sai dai ba da jimawa ba ’yan ta’addan suka yi garkuwa da direbobin tare da fasinjojinsu.
Majiyar leken asirin ta Zagazola Makama, kwararren mai fashi baki kan harkokin tsaro da tayar da kayar baya a Tafkin Chadi, ta bayyana cewa sojoji sun kai wa wadanda abin ya shafa dauki cikin gaggawa.
A cewar majiyar, “bayan samun kiran na gaggawa, sojojin 112 Task Force Battalion Mafa tare da hadin gwiwar Civilian JTF da mafarauta sun tashi daga Mafa suka nufi kauyen Gullo don neman wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 1 ga Yuni, 2023.
Majiyar ta ce “da ganin sojojin na OPHK ne sai nan da nan ‘yan ta’addan suka yi watsi da wadannan direbobin da suka yi garkuwa da su, suka tsere.
Ta kara da cewa,“ sojojin sun samu nasarar kubutar da wadanda lamarin ya shafa bayan sun raraka mayakan wadanda suka gudu suka bar ladansu.”