✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cakfe Sunday Igboho yana kokarin tserewa zuwa Jamus

An dai cafke shi ne a birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin.

Hukumar Tsaro ta DSS ta cafke mutumin da ke ikirarin jagorantar yunkurin ballewar Yarabawa daga Najeriya, Sunday Igboho.

DSS ta cafke Igboho wanda take nema ruwa a jallo ne a lokacin da yake kokarin tserewa daga Najeriya zuwa kasar Jamus.

Kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta rawaito cewa an cafke shi ne a birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin, a daidai lokacin da yake kokarin guduwa kasar ta Jamus.

Kafar ta kuma rawaito cewa jami’an tsaron kasar ne suka kama shi, kuma ana sa ran za a dawo da shi Najeriya kowanne lokaci daga yanzu.

Kokarin Aminiya na jin ta bakin Kakakin Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, Peter Afunanya ya ci tura saboda bai daga kira ko amsa wayar da wakilinmu ya yi masa ba.

A ranar daya ga watan Yulin 2021 ne hukumar ta DSS ta ayyana neman Igbohon ruwa a jallo.

Yaran Igbohon biyu dai sun rasa ransu bayan wata musayar wuta da jami’an tsaro a gidansa, yayin da aka kama mutum 12 da tarin makamai lokacin da aka kai masa hari.

Yayin wani taron manema labarai a shalkwatar DSS dai, Peter Afunanya ya lashi takobin cewa DSS za ta kama Igboho.