✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke ’yan uwa da jaka 49 na tabar Wiwi a Kano

"Mahaifina ya kai shekara 20 yana dillacin tabar wiwi", cewar matashin da 'yan sanda suka cafke.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani matashi mai shekara 21 da wasu jakunkunan tabar Wiwi 49, wanda ya ce na mahaifinsa ne.

An kama matashin ne yayin da yake kokarin kwashe jakunkunan zuwa inda zai boye su.

“Bayan Kwamishinan ’Yan Sandan jihar,  Habu Sani ya ba da umarnin bincike, Shugaban Sashin Ayyukan ’Yan-daba, Bashir Mubammad Gwadabe ya kamo wanda ake zargin”, cewar Kiyawa.

Ya ce nn kama wanda ake zargin ne yayin da yake kokarin boye yabar Wiwin.

Ya kara da cewa an cafke mahaifiya da kawun wanda ake zargin a unguwar Gadon Kaya da ke Kano.

Matashin ya bayyana wa ’yan sanda cewa mahaifiyarsa ce ta sanar da shi an kama mahaifinsa, ta kuma umarce ya je ya boye ragowar tabar wiwin.

Bayan cafke sa a unguwar Danbare, inda yake kokarin boye Tabar a gidan abokinsa, ya ce mahaifinsa ya dauki tsawon shekaru 20 yana harkar Tabar Wiwi.

Kiyawa ya ce Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya ba wa sashen binciken cikin gida don gano ta inda ake shigo da Tabar zuwa Kano.