Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da cafke wasu mutum uku da ake zargi da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a Jihar Adamawa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje ne ya sanar da hakan yayin zanta wa da manema labarai cikin birnin Yola a ranar Lahadi.
- Saura kiris jam’iyyar APC ta rushe – Tambuwal
- Coronavirus ta yi ajalin mutum 3 a Najeriya, 112 sun kamu
- Za a fafata yakin basasa muddin aka kashe Gwamnan Binuwe – Wike
Nguroje ya ce an cafke ababen zargin ne a maboya daban-daban da ke kauyukan Muleng da Chigari na Kananan Hukumomin Song da Fufore.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito, rundunar ’yan sandan ta samu nasarar cafke miyagun ne bayan tattara bayanan sirri da kuma tsananta sintiri da bincike da suka yi tare da hadin gwiwar kungiyar ’yan sa kai.
Kakakin ’yan sandan ya ce wadanda ake zargi su ne a watan Mayun da ya gabata suka yi garkuwa da shugaban wata makarantar koyon sana’ar hannu, Mista Elan Jobbo da Jabbi Lamba da Alhaji Jauro Mamburso da Alkani Zumbe, dukkansu a Kananan Hukumomin Girei da Song.
“Ababen zargin da suka shiga hannu sun hada da Usman Sale mai shekara 40 mazaunin kauyen Muleng, Lawali Sale mai shekara 37 da Yerima Dadi mai shekara 36 mazauna kauyen Bah Usman.”
“Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa ababen zargin suna da hannu a ayyukan fashi da makami da satar mutane da ke aukuwa a kan iyakar Najeriya da Kasar Kamaru.”
“Kwamishinan ’yan sanda CP Aliyu Aliyu yayin da yake yabawa DPO na Song da jami’ansa, ya kuma ba da umarnin ci gaba da bincike a kan lamarin domin samun karin hujjojin gurfanar da ababen zargin yadda ya kamata,” in ji Nguroje.