Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) ta cafke wasu matasa biyu ’yan bumburutun dauke da manyan jarkoki 30 na man fetur a Jihar Kwara.
Kamun matasan ya biyo bayan karancin man fetur da ake tsaka da fama da shi a fadin tarayyar kasar nan.
- Sumayya Shu’aibu: Budurwar da ta rubuce Al-Qur’ani cikin watanni 3 a Zariya
- Rikicin APC: Ganduje ya kayar da Shekarau a Kotun Daukaka Kara
A cewar kakakin NSCDC na jihar, Babawale Zaid Afolabi, ya ce an cafke matasan ne da jarka 30 na man fetur da suka sayo a wata jiha don sayarwa da tsada a jihar.
“Tawagar jami’anmu ta musamman karkashin jagorancin Ayinde Yusuf ta kama wata motar haya makare da jarka 30 na man fetur,” cewar Babawale.
Ya bayyana cewa ’yan bumburutun da ake zargin sun amsa cewa suna sayo man fetur din ne daga garin Ogbomoso na Jihar Oyo, suna sayarwa a farashi mai tsada ga masu ababen hawa a Ilorin.
A cewarsa, hukumar na kokarin hana a jefa al’umma cikin mawuyacin hali musamman a lokacin da ake fuskantar karancin man fetur a jihar da ma kasa baki daya.
Ya ce hukumar za ta gudanar da bincike kafin ta amika matasan a gaban kotu don yanke musu hukuncin da ya dace da su.