Yaya za ka ji a ranka, bayan ka gama bin layin karbar katin zabe, sai da aka zo kanka, aka duba ‘list’ aka ga sunanka da sauran bayanaka, amma aka nemi katin naka sama da kasa aka rasa?
To dubun wani mutum ta cika, inda aka kama shi dauke da katunan masu zabe sama da guda 100, kuma ya kasa bayanin daga inda ya samo su.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sauya Takardun Naira Za Ta Shafe Ku
- Fargabar Hari: Sufeton ’Yan Sanda Ya Ba da Lambobin Kiran Gaggawa
Mutumin ya shiga hannu ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), take shirin fara raba ’yan Najeriya da suka yi rajista a karon farko ko suka sabunta katunansu a gabanin zaben 2023.
’Yan sanda sun ce bisa dukkan alamu wanda ake zargin ya tattaro katunan zaben ne daga jihohi daban-daban.
’Yan sanda sun cukwikuye shi ne bayan asirinsa ya cika a yankin Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato inda aka same shi da katunan zabe guda 101.
Sabon Birni na daga cikin kananan hukumomin jihar da ke fama da matsalar tsaro.
Yadda za mu yi da katunan —’Yan sanda
Da yake magana kan cafke mutumin, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Hussain Gumel, ya bukaci al’umma, musamman wadanda katin zabensu ya bace, su ziyarci babban ofishin rundunar don bincikawa.
Haka nan, ya ba da tabbacin za su kwashi ragowar katuttukan da ba a gano masu su ba a maida su Ofishin Hukumar Zabe (INEC).
Wannan rahoto na zuwa ne kwanaki kadan bayan INEC ta fitar da alkaluman rukunin karshe na mutane da ta yi wa rajistar zabe a fadin Najeriya.
Kasuwancin katin zabe
A ’yan kwanaki baya, rahotanni suna nuna kama wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano da katunan zabe guda 367 wadanda ya kasa bayanin yadda ya samo su.
Matsalar sayar da katunan zabe ko kuri’a na daga cikin abubuwan da har yanzu ke ci wa tsarin zaben Najeriya tuwo a kwarya.
A lokuta da dama akan kama masu bi gidaje a birane ko kauyuka suna yi wa mutane romon baka domin su sayar musu da katunansu na zabe — wanda yin hakan laifi ne a karkashin dokar zabe.
A wasu lokuta kuma, ana zargin har sace wa mutane katunan zabe ake yi a sayar wa ’yan siyasa domin su yi amfani da su wajen yin magudi a lokacin zabe.
A wani salo kuma, ’yan siyasa kan yi irin haka ne a wuraren da abokan adawar abokan hamayyarsu ke da karfin goyon baya, da nufin gurgunta tasirin abokan adawar tasu a akwatin zabe.
Ungulu da kan zabo a jefa kuri’a
Bata-garin ’yan siyasar kuma kan yin amfani da irin wadannan katunan da suka saya wajen yin magudi ta hanyar jefa kuri’a.
Sukan yi haka ne ta hanyar amfani da ’yan barandarsu, da ke zuwa rumfar zabe su yi sojan gona cewa sai an sun jefa kuri’a da katunan.
Suna fakewa ne da dokar zabe da ta ba da dama idan na’urar tantance mutane ba ta dauki zanen yatsu ba, a cike masa takardar (Incident Form) a bari ya jefa kuri’a.
Sabuwar dokar zabe
Sai dai sabuwar dokar zabe ta soke amfani da fom din, ta kuma tanadi da amfani da na’urar BVAS, wadda za ta rika tantance masu kada kuri’a ta hanyar daukar hotonsu da kuma zanen yatsunsu.
’Yan Najerya dai na kyautata zaton amfani da BVAS zai yi wa wannan tufkar hanci.
Amma abin tambaya shi ne zuwa yaushe ko a wane mataki? Saboda a duk lokacin da INEC ta bullo da wata fasahar dakile magudi, sai miyagun ’yan siyasa sun yi kokarin ganin yadda za su kauce masa domin cim-ma muguwar manufarsu.
A gaya da dokar zabe ta tanadi amfani da na’urar tantance masu zabe, an yi zaton matsalar za ta kau, amma sai bata-garin ’yan siyasa suka rika fakewa da damar amfani da Incident Form su yi magudi.
Abin jira a gani shi ne yadda zaben 2023 zai gudana kuma tasirin da tsarin BVAS zai yi.