✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke wani da buhu 45 na miyagun kwayoyi a Katsina

Rundunar ta ce za ta mika wanda ake zargin ga NDLEA.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani mutum da buhu 45 na kayan maye.

Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai shekarua 30 ne a Malumfashi.

A cewarsa, abubuwan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da kwalabe 500 na magungunan maye da wasu allursi.

“A ranar 3 ga watan Janairu, 2024, bisa sahihan bayanan sirri da muka samu daga wata majiya mai tushe, rundunar ta yi nasarar kama wanda ake zargin a Malumfashi.” in ji jami’in.

Ya kara da cewa a yayin binciken wanda ake zargin an kai ga gano wasu haramtattun miyagun kwayoyi.

Kakakin ya bayyana cewa wanda ake zargin wanda dillalin kwayoyi ne, ya tabbatar da mallakar buhu 45 na miyagun kwayoyin.

Sadiq-Aliyu ya bayyana cewa yayin bincike an gano wasu mutum biyu da ke taimaka masa wajen safarar miyagun kwayoyin.

“A halin yanzu, za a mika wanda ake zargi ga hukumar NDLEA don ci gaba da bincike,” in ji shi.