A ranar 26 ga Disamba 2020, rundunar ’yan sandan Kaduna ta kame wasu matasa da suka shirya casun tsiraici a garin Kaduna.
Masu shirya casun sun tsara shi ne ta yadda mahalarta maza da mata za su kasance tsirara, kuma masu sha’awar yin jima’i a wurin casun na da damar yin hakan.
- An kashe ’yan bindiga 9 a hanyar Kaduna-Abuja
- Tankar mai ta kama da wuta a hanyar Kaduna-Zariya
- ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa a kauyen Kaduna
Kakakin rundunar, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da cewa jami’ansu sun gano wajen casun, inda a nan suka kame wadanda suka shirya taron badalar.
Sai dai bai bayyana adadin mutanen da suka cafke a wajen taron ba, amma ya ce ana yin bincike kuma da zarar an kammala zai ba da sanarwa.
Wakilinmu ya ce matasan sun shirya gudanar da casun jima’in na farko ne a ranar 27 ga Disamba 2020, wanda suka tallata ta kafafen sa da zumunta, amma ba su bayyana inda za su yi taron ba.
An shirya fara gudanar da taron da misalin karfe 8 na dare har zuwa wayewar gari.
Katin gayyatar taron ya nuna cewa za mahalarta na gama-gari za su biya N2000, sai kuma N3,000 da N5,000 ga mahalarta na musamman.