✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke uba ya yi wa ’ya’yansa uku fyade

Kotu tsare magidanci da ya yi lalata da ’ya’yan cikinsa uku.

Kotu ta tisa keyar wani magidanci da aka kama ya yi lalata da ’ya’yan cikinsa mata guda uku.

Jami’an tsaron hukumar Sibil Defens sun cafke mutum ne bayan samun labarin tsiyar da yake aikatawa.

Kakakin hukumar a Jihar Anambra, Edwin Okadigbo ya ce “Bayan kammala bincike an gurfanar da mutumin a Babbar Kotun Jihar kuma Alkalin ya tura shi zuwa Gidan Yari ta Awka.”

Magidancin, mai shekara 48 ya amsa cewa ya yi wa ’ya’yan nasa fyade, wanda ya ce sharrin giyar da yake sha ne.

Daga nan Kotun ta ba da umarnin a tsare shi a gidan yari