Sojoji sun cafke hatsabibin jagoran ’yan bindigar da ke fitinar kananan hukumomi uku a Jihar Neja, wanda ake wa lakakbi da Jack Bros Yellow.
An kama Jack Bros Yellow ne a yayin da sojoji ke ci gaba da sharar dazukan Jihar Neja da nufin tarwatsa maboyan ’yan bindiga da ke hana al’ummomi sakat.
- Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa
- Yadda aka yi Hawan Sallah a Fadar Sarkin Zazzau
- Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi a Kaduna
- Yadda fasto ‘ya babbake’ miloniya yayin yi masa addu’a
Majiyarmu ta an kama Jack Bros Yellow ne a dajin tsakanin kananan hukumomin Shiroro da Rafi a wani samame na sirri da sojoji suke yi don guje wa manakisar masu kai wa bata-garin bayanai.
Hukumomin soji ba su sanar da hakan ba, amma majiyarmu ta ce kame Jack da aka yi ya karya lagon ayyukan ’yan bindiga a yankin a cikin mako daya da ya gabata, inda yaransa ke sulalewa.
“Jack Bros Yellow ne shugaban daya daga cikin gungu uku na ’yan bindiga da ke aiki a yankin Kananan Hukumomin Shiroro, Rafi da Munya.
“Yana cikin wadanda suka sa wasu al’ummomi biyan Naira miliyan uku kafin su zauna lafiya amma da aka biya kudin sai sauran suka cuce shi.
“Sai ya je da yaranshi suka kwashi wasu mata kusan tara a kauyen Galape, gaba da Galkogo a Karamar Hukumar Shiroro a watan Janairun bana.
“Tun ranar 5 ga Janairu har zuwa lokacin da aka tsare shi a makon jiya matan ke hannunsa yana neman kudin fansa Naira miliyan 10, amma har yanzu ba mu ga matan ba tukuna,” inji majiyarmu.
Wata majiya ta ce Jack Bros Yellow na da alaka da wasu ’yan bindiga a Zamfara wadanda yake kai musu ajiyar mutanen da ya yi garkuwa da su da ba a biya kudin fansarsu da wuri ba.