Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, ta cafke wasu mutum biyu da bindigogin AK-47 guda 27 kirar gida a Karamar Hukumar Kontagora ta Jihar Neja.
Mukaddashin Kwamandan Hukumar reshen Jihar, Mista Isaac Aloye ne ya sanar da hakan yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Minna, babban birnin Jihar a ranar Talata.
- Buhari ya haramta tashi da saukar jirage a Zamfara
- Abin da nake son sauyawa a Kannywood —Stella Dadin Kowa
- Obasanjo ya shiga bayan labule da kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP
Mista Aloye ya ce an cafke ababen zargin biyu da manyan bindigogi 12 kirar gida da kuma kanana 15 a kan babbar hanyar Kontagora zuwa Mashegu.
“Jami’anmu sun kama mutanen biyu yayin da suka dauko dakon bindigogin a cikin wani farin buhu haye a kan wani babur,” in ji shi.
Ya ce binciken somin tabi da suka gudanar ya nuna musu cewa makerin bindigogin mazaunin kauyen Kampani ne da ke Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar.
Ya kara da cewa, an kera kowace bindigar AK-47 a kan Naira dubu biyar yayin da aka kere kowace karamar bindigar irin ta ‘saka ni a wando ka saya ni’ a kan Naira dubu uku.
“Za mu mika wa rundunar ’yan sandan Minna ababen zargin domin ci gaba da bincike,” a cewar Mista Aloye.