✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke matar aure tana sayar da dan kishiyarta

Dubunta ta cika a lokacin da take kokarin sayar da yaron a Gusau, Jihar Zamfara

’Yan sanda sun cafke wata matar aure ’yar kasar Jamhuriyar Nijar tana kokarin sayar dan kishiyarta mai shekara biyu a Jihar Zamfara.

Kamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ayuna Elkanah, ya ce dubun matar ta cika ne a lokacin da take kokarin sayar da yaron a unguwar Tullukawa da ke garin Gusau, Babban birnin Jihar Zamfara.

Ya ce bayan an kama matar, wadda ta fito daga kuayen Danayde Kaya da ke Jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar, ta bayyana cewa ta sace yaron ne domin ta sayar da shi a matsayin ramuwar gayya kan sace da kishiyarta ta yi ta kuma sayar.

Ta kuma bayyana cewa ta sace yaron za ta sayar da shi ne domin ta samu kudin yin hidindimunta na yau da kullum.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce nan gaba za a mika matar ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya domin daukar mtakin da ya dace a kanta.

Da yake bayani, ya bayyana cewa sojojin da aka girke a kan hanyar Dansadau da ke  Karamar Hukumar Maru ta jihar sun dakile wani hari tare da kubutar da mutum 17 da aka yi garkuwa da su daga kauyen Wamba na Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja a ranar 14 ga watan Disamban 2021.

An mika mutanen da aka kubutar din ne ga Rundunar Soji ta Daya, inda aka duba lafiyarsu sannan aka mika su ga ’yan sanda domin mika su ga iyalansu.