Hadin gwiwar jami’an tsaron Operation Safe Haven sun kame mutum 23 da ake zargi da aikata fashi da garkuwa da mutane.
Kwamandan Rundunar, Manjo-Janar Dominic Onyemelu, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da wandada ake zargin ga manema labarai a Jos.
- Jam’iyyar APC da kara wa’adin rajistar mambobinta
- Za a ci gaba rajistar masu zabe 28 ga watan Yuni —INEC
- An kama matashi mai kai wa Boko Haram kwayoyi
- An yi gobara a kasuwar Doya a Filato
“Wadanda aka cafke din an same su dauke da muggan makamai da suek amfani da su wajen aikata laifuka daban-daban,” a cewar Onyemelu.
Ya ce 17 daga cikin wadanda aka cafke din, ana zargin su da laifin yin garkuwa da mutane, hudu kuma laifin fashi da makami, sai ragowar biyun da ake zargi da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Onyemelu, ya ce dole ne sai mutane sun taimaki jami’an tsaro, sannan za rika samun nasarar dakile miyagun ayyukan bata-gari.