✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke mai yi wa Boko Haram safarar fetur

An kwato motoci uku da ake zargin yana safarar fetur da su ga Boko Haram.

Dakarun Operation “Hadin Kai” tare da hadin gwiwar ’yan banga sun cafke wanda ake zargi da yi wa kungiyar Boko Haram safarar kayan amfanin yau da kullum a garin Kurkareta da ke Jihar Yobe.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwar da Daraktan Yada Labaran Sojin, Brigediya Mohammed Yerima, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

“Dukkannin kayan da aka samu daga wajen wanda ake zargin mun ajiye su a wajenmu don fadada bincike, kafin mika su ga hukumomin da suka dace.

“Rundunar Soji ta yi nasarar dakile yunkurin kai hare-hare a yankin.

“Muna tabbatar wa jama’a cewa za mu ci gaba da kare rayukansu da dukiyoyinsu daga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran bata-gari a yankin Arewa-maso-Gabas da ma kasa baki daya,” kamar yadda ya bayyana.

Yerima ya kara da cewar an samu manya-manyan duro guda 62 cike da man fetur da aka boye a gidaje da shaguna daban-daban.

Kazalika an kwato motoci uku wadanda ake zargin da su yake safarar kayayyaki ga Boko Haram a jihar.

Yerima, ya kara da cewa samamen nasu ya yi nasara ne bayan samun bayanai daga wasu mutane kan wanda ake zargin.