An cafke wani likita mai kan zargin cire sassan jikin marasa lafiyan da yake dubawa domin sayarwa da kuma garkuwa da mutane.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kwara, Paul Odama, ya ce dubun likitan da ake zargi ta cika ne a lokacin da yake kokarin sayar da motar daya daga cikin marasa lafiyan da yake dubawa.
- ’Yan sanda sun kama ’yan fashi da dillalin kwaya a Jigawa
- DSS ta tsananta binciken Emefiele kan daukar nauyin ta’addanci
Ya a bayyana wa manema labarai a ranar Litinin, cewa jami’an tsaro sun bankado yadda wanda ake zargin ya kashe wata mata a otal, kuma, “Ya bayyana yadda ya yaudari wata ya cire mata wani sashe na jikinta.
“Sannan ya amsa kashe wata mai suna Olanipekun Ifeoluwa Ibukun, wadda ya buge ta wani abu a kanta sannan ya jefar gawar a daji a yankin Alapa.
“Ya kuma amsa laifin garkuwa da wani mai suna Malam Abubakar da wata ma’aikaciyar asibitin Kaiama, Nafisat Halidu, wadda ya rufe ta a wani ofis a asibitin ba tare sa kowa ya sani ba.
“Sannan ya amsa kashe wata mata tare sa binne gawarta a dakin ajiya a asibitin.
“Gaba daya an tono gawar mutum shida da ake zargin ya kashe, an ajiye su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin don gudanar da bincike.”
Sai dai a lokacin da aka gabatar da shi ga manema labarai, likitan da ake zargi ya musanta dukkan laifukan da ake tuhumar sa da su, inda ya ce tilasta shi aka yi ya amsa cewa ya aikata.