✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane

Daga cikin wadanda aka kama din har da ma’aikaci dake aiki a sashen tsaro na jmai’ar mai suna Aliyu Abubakar.

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Najeriya sun cafke wasu da ake zargi da hada baki ana yin garkuwa da mutane a daya daga cikin manyan jami’o’in Najeriya, Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Daga cikin wadanda aka kama din har da ma’aikaci da ke aiki a sashen tsaro na Jmai’ar.

Dakarun Runduna ta Musamman da ke aiki karkashin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya ne dai suka cafke shi, kuma ana zargin sa da taimaka wa masu garkuwar da suka addabi Jami’ar a lokuta daban-daban.

Kakakin rundunar, DCP Frank Mba ne ya sanar da hakan a yayin ci gaba da bajekolin masu laifukan taimaka wa masu garkuwar.

Kazalika, ya kuma ce sun samu nasarar kama wani mai suna Malam Jafaru wanda ya kware wajen hada wa masu satar mutanen asirin samun sa’a.