✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke fasto kan yi wa karamar yarinya fyade

’Yan sanda sun cafke wani limamin coki kan zargin yi wa wata karamar yarinya fyade

’Yan sanda sun cafke wani fasto mai shekaru 43 kan zargin sa da yi wa wata karamar yarinya fyade.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta damke Fasto Clinton John da ke cocin Mega Healing Ministry ne bayan mahaifan yarinyar sun kawo karar sa kan abin da ke faruwa.

Kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ta ce iyayen yarinyar ’yar shekara 16 sun yi zargin akwai rina a kaba ne bayan ’yar tasu ta fara nuna wasu sabbin halaye, ga muka fama da lalura a matuncinta.

Ta bayyana cewa bayan an yi ta faman magani ne ’yar ta shaida musu cewa wani ne ya yi mata fyade kuma ya yi barazanar zai kashe ta idan ta kuskura ta fada wa wani.

SP Odutola ta ce yarinyar ta shaida musu cewa tun a watan Nuwamban 2022 Fasto Clinton yake wannan aika-aika, amma tana tsoron ta fada wa wani, saboda barazanar kashe ta da ya yi.

Daga karshe da kyar mahaifan suka lallashe ta, sannan ta bayyana musu cewa Fasto Clinton na cocin Mega Healing Ministry ne.

Odutola ta ce a yayin bincike, Fasto Clinton  ya amsa cewa ya sha yi wa yarinyar fyade; Za a kai shi babban ofishin sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike a kansa.
Ita kuma yarinyar an kai ta asibiti domin kara duba ta.