Wata mota ta yi yunkurin kutsawa cikin masallacin Ka’aba inda ta dangane da kofar shiga masallacin ta 89.
Kamfanin Dillancin Labaran kasar Saudiyya, ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Juma’a.
- Maniyyata Umrah za su fara isa Saudiyya ranar Lahadi
- Saudiyya ta yi wa musulmi albishir kan aikin Umarah
Rahoton ya ce na’urar CCTV ta dauki hoton motar yayin da take yunkurin kutsa kai cikin ginin masallacin.
Sai dai hukumomi sun bayyana cewa babu wanda ya jikkata, sannan kuma an kama direban nan take.
Wasu hotuna sun nuna yadda aka daure hannayensa kafin a fita da shi.
Direban motar da aka kama dan asalin kasar Saudiyya ne, kuma alamu sun nuna cewa yana cikin yanayin tabin hankali.
Jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi domin gudanar da bincike a kansa.