’Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke wasu mutum hudu da suka kware wajen sayar da makamai ga masu aikata laifuka a Jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sanusi Buba ne ya bayyana hakan yayin gabatar wa manema labarai muggan makaman da suka kama, inda ya ce sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne baya samun bayanan sirri.
- An kubutar da ’yan Kasar Nijar 9 daga hannun masu garkuwa a Jihar Katsina
- Dan sanda na barazana ga wakilin Daily Trust a Katsina
- An ceoto mutum 77 daga masu garkuwa a Katsina
“Bayanan sirrin da muka samu sun taikama mana wajen kamo wani mutum mai shekar 35 a kauyen Maduru da ke Karamar Hukumar Mani a Katsina.
“Mutumin ya kware wajen safarar makamai ga masu aikata laifi a Katsina da wasu jihohi makwabta.
“A yayin bincike kuma mun sake gano mutum uku da ke taimaka masa wajen safarar makaman, a kauyukan Sawarya da kuma Maduru.
Daya daga cikin mutanen ya amsa cewar shi ne shugabansu kuma ya dade yana fasakwaurin makamai har zuwa Jamhuriyyar Nijar.
Sannan ya bayyana cewa ba zai iya tuna adadin makaman da sayar wa masu aikata laifuka ba, amma a cewarsa ya sayar da makamai sama da 10,000.
Mutum biyun da ke taimaka masa kuma sun bayyana wa ’yan sanda cewa su ne suke kai makamai yankunan Gurbi da Dan-Magaji da ke Jihar Zamfara.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya kara da cewa an samu muggan makamai da suka hada da manyan bindigu, harsasai da tulin kudi da suka kai Naira miliyan 3.4 a hannun wadanda ake zargin.