✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke dan damfarar na’urar ATM a Katsina

Nakan tsaya a bakin banki domin samun wadanda ba su kware ba wajen amfani da na’urar ATM.

‘Yan sanda sun kame wani matashi da ake zargi yana dan damfarar mutane da katin banki na na’urar ATM a Katsina.

Matashin mai shekara 21 wanda haifaffen garin Funtuwa ne a Karamar Hukumar Funtuwa da ke Jihar Katsinan, ya kware wajen yaudarar mutanen da ke neman taimakon yadda za su yi amfanin da na’urar ATM.

Ya fada komar ‘yan sanda bayan ya gamu da bacin rana yayin da yake rike da katukan ATM na bankuna daban-daban.

A cewar matashin, yakan tsaya a bakin banki domin samun irin mutanen da ba su kware a wajen cire kudi ta na’urar ATM ba wadanda ke neman taimakon wadansu domin cire kudi. 

Ya shaida wa Aminiya cewa: “Maimakon na yi amfani da katin da mutum ya ba ni, nakan fakaici idonsa na musanya da wani.

“Sai in sanya na hannuna irin wanda mai bukatar taimakon ya zo da shi, na sanya cikin na’urar. 

“Bayan na tambayi lambar sirrin katin, karshe zan fitar da kati da na sanya na hannuna da cewa, akwai matsala ba za a iya fitar da kudin ba a lokacin. 

“Sai bayan mai katin ya tafi zan fito da wancan na cire dukkan kudaden da na samu cikin asusun bankin,” a cewar sa.

Ya ce yana zuwa ne daga garin Funtuwa zuwa Katsina kacokan domin wannan harkar, kuma yakan tafi wurare daban daban don cire kudaden. 

A cewarsa, a wannan harkar ya cire kudaden jama’a sama da N1m a cikin wata uku da suka wuce.

Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar, SP Gambo Isa ya ce suna ci gaba da binciken lamarin. 

Sannan ya yi kira musamman ga masu zuwa bankuna don cire kudade da su rika sanin wadanda za su nemi taimakonsu domin kaucewa fadawa hannun bata-gari.