✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bullo da sabuwar hanyar gwajin Coronavirus a Ogun

Gwamnatin jihar Ogun ta bullo da sabon salon gwajin coronavirus tayin amfanin da gidan gilashi wanda masana kiwon lafiya a jihar suka ce hanya ce…

Gwamnatin jihar Ogun ta bullo da sabon salon gwajin coronavirus tayin amfanin da gidan gilashi wanda masana kiwon lafiya a jihar suka ce hanya ce da zata baiwa ja’mian kiwon lafiya kariya fiye da rigar silken kariyar annobar da ake amfani da ita.

Gidan gilashin wanda jami’an kiwon lafiyan kan kasance daga ciki yayin da wanda za a yiwa gwajin ke tsayawa a daya bangaren ta yadda jami’an kiwon lafiyan za su zuraro hannu sanye da Safar hannu ta robo a wata kafa inda zasu dauki samfurin daga jikin wanda za a yiwa gwajin ta kafar hancinsa.

Tuni dai aka fara amfani da wannan sabon salo a cibiyar gwajin masu cutar da ke yankin Ijamido a Sango Ota.
Mataimakiyar Gwamnan jihar Ogun No’imot Salako ta bayyana haka a lokacin da takai wa cibiyar ziyarar gani da ido tare da kwamishinan lafiya na jihar Dakta Tomi Coker Wanda ya shaida cewa wannan sabuwar hanya ce mai saukin hatsari ga jami’an kiwon lafiya.

A cewar ma’aikatar lafiya a jihar Ogun, gidan gilashi wanda shine irin sa na farko a Najeriya yafi tabbas idan an kwatanta shi da rigar kariya da jami’an kiwon lafiya ke sanya wa domin akwai hadarin daukar cutar a lokacin da mai sanye da rigar ke kokarin cire rigar daga jikinsa.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan lafiya arba’in da biyu ne suka kamu da coronavirus a Najeriya yayin da biyu suka mutu a sakamakon cutar.

 

Wani Jami’in kiwon lafiya daga cikin gidan gilashi yana daukar samfurin daga jikin wata mace da ake wa gwajin coronavirus a Ogun