✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci Shugaba Buhari ya nemo mashawarta masu kishin kasa

Tsohon Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa [NURTW] reshen tashar motar Bauchi road da ke garin Jos, Jihar Filato, Alhaji Habibu Abubakar ya yi kira ga…

Tsohon Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa [NURTW] reshen tashar motar Bauchi road da ke garin Jos, Jihar Filato, Alhaji Habibu Abubakar ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya nemo masana tattalin arziki nagari masu kishin kasa da za su rika ba shi shawarwari nagari kan farfado da tattalin arzikin kasar nan musamman a bangaren harkokin kasuwanci, a sabuwar gwamnatin da zai kafa.

Shugaban yi wannan kiran ne a lokacin da yake zanta wa da jaridar Aminiya a garin Jos,

Ya ce a wannan wa’adin shugabanci na Shugaban Kasa Buhari mai kerewa, shugaban bai samu masu ba shi shawara nagari kan tattalin arziki ba.  Kuma yawancinsu ba masu kishin talakawa ba ne, kawai dai masu kishin kansu ne kawai.

Ya kara da cewa a duk wata kasa ta duniya ana takama ne da ’yan kasuwa. Amma sakamakon irin shawarwarin da masu bai wa wannan gwamnati ta Shugaba Buhari shawara kan tattalin arziki, sai ya kasance a shekara 4 da ta yi tana mulkin kasar nan, ta karya ’yan kasuwar kasar nan da dama domin duk wani dan kasuwa a karkashin wannan gwamnati ya ji a jikinsa.

Ya ce misali a nan Najeriya kowanne yanki akwai irin arzikin da Allah Ya ba suinda ya nuna cewa, “yankin Arewacin Najeriya Allah Ya ba mu arzikin makwabta da wasu kasashe da muke shige da fice, muna samun abin da za mu ci tsakaninmu da su.”

Har’ila yau ya ce yankin Kudu maso Kudu suna da mai kuma suna nan suna gudanar da harkokinsu na mai. Yankin Kudu masa Yamma kuma suna da tashoshin teku, suma nan suna harkokinsu na shigo da kayayyaki daga kasashen waje.

“Amma yankin Arewacin Najeriya an zo an rufe mana iyakokin kasashen da muke makwabtaka da su. Yanzu a Arewa jami’in kwastan idan ya kama ka dauko buhun shinkafa daya, zai iya sa bindiga ya harbe ka. Amma a Legas sai a sauke tirela 1000 na shinkafa, babu wanda zai kama ka.”

Don haka ya yi  kira ga Buhari da ya nemo masana tattalin arzikin kasa masu basira da kishin kasa, domin a cewarsa wasu daga cikin masu ba shi shawara na yanzu ba taimaka masa suke yi ba, suna rusa masa gwamnati ne.