✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci musulmi su rika taimaka wa addini

Reshen kungiyar Izala ta kasa mai hedkwata Jos da ke Kalaba Jihar Kurosriba ya bukaci al’ummar Musulmi da su zuba jari wanda babu kamarsa wajen…

Reshen kungiyar Izala ta kasa mai hedkwata Jos da ke Kalaba Jihar Kurosriba ya bukaci al’ummar Musulmi da su zuba jari wanda babu kamarsa wajen raya ilmi da kuma karantarwa da karatu.

Alhaji Sale Suleiman Jimeta, shugaban kungiyar na jihar ne ya bukaci haka, a lokacin da suka zanta da Aminiya jim kadan da kungiyar ta gudanar da neman gudunmawar tallafa wa ilmi da aka yi.

Shugaban Jibwis na Kurosriba ya ci gaba da cewa: “Ka san neman ilimi wajibi ne ga kowane Musulmi, zama da jahilci ba hanzari ba ne ga Musulmi. Shi ya sa ma Allah Madaukakin Sarki Ya ce ‘ku yi karatu’ ‘ka san ni kafin ka bauta mini.”

Da aka tambaye shi ko me ya sa Jibwis ta fi mayar da hankali wajen fifita gidauniyar neman ilmi alhali ga mabukata irin matan da aka mutu aka bar musu marayu da kuma ’yan gudun hijira, a nan sai ya kara da cewa: “Ana yi, domin wani lokaci in an yi neman taimakon su ma ana yi masu, ana kuma taimaka musu amma dai wannan neman ilmi shi ne mutane suka fi mayar da hankali gare shi; galibi kuma sauran gwamnati kan rika daukar nauyinsu.”

Akalla kimanin Naira milyan daya da rabi ake fata a samu gudunmawa a asusun na raya ilmi da ilmantarwa daga kungiyar reshen Jihar Kurosriba. Daga karshe ya nemi al’ummar Musulmi da su fito su taimaki Musulunci da Musulmi domin daukakarsa da komai kankantar abin da Allah Ya huwace wa mutum, ba sai lallai mutum ya bayar da wasu makudan kudi ba. Ya yi addu’ar Allah Ya kara wanzar da zaman lafiya a Najeriya.