✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci diyya kan barnar da a ka yi wa ‘yan Arewa a Kudu

Gammayyar Kungiyoyin Matasan Arewacin Najeriya mai suna Coalition of Northern Group a harshen Ingilishi, ta bukaci diyya kan barna da a ka yi wa ‘yan…

Gammayyar Kungiyoyin Matasan Arewacin Najeriya mai suna Coalition of Northern Group a harshen Ingilishi, ta bukaci diyya kan barna da a ka yi wa ‘yan yankin a kudancin Najeriya a lokacin zanga-zangar neman kawo karshen rundunar tsaron ‘yan sanda ta #EndSARS da ta rikide ta koma tarzoma.

Mai magana da yawun kungiyar Malam Sulaiman Abdul’aziz wanda ya bayyana bukatar kungiyar a yayin zanta wa da ‘yan jarida a ranar Litinin a birnin Abuja, ya kuma yi zargin watsi da abin da ya faru ga ‘yankin tare da yayata na wani bangare guda kadai.

Kungiyar ta ce da gangan gwamnatocin kasashe da hukumomin duniya musamman masu hakkin bil’adama ba su ce uffan a kan barnar da ya shafi al’ummar yankin ba.

Sulaiman Abdul’aziz ya ce kungiyar ta fara aikin tattara adadin barnar da a ka yi wa al’ummar Arewacin Najeriya a garin Aba na jihar Abiya da jihar Imo da Ribas da Legas da dai sauransu.

Ya ce za su mika kundin bayanin ga kungiyar Gwamnonin Arewa da nufin mika shi ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da neman diyya a kai, kamar yadda ya ce wasu gwamnoni daga kudancin kasar nan, su ka nema wa ‘yan yankinsu, inji shi.

Kazalika ya ce sun mika takardar korafi ga Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai, sai kuma Ofisoshin Jakadanci na kasashen Birtaniya da Israila da kuma Kanada kan aikace-aikacen kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara wato IPOB, da ya zarga da kitsa barnar.

Kungiyar matasan arewa ta ce hakan ya zama dole ganin yadda kasashe ukun su ka bayar da mafaka ga jagoran kungiyar tare da bashi damar kafa gidan rediyo da ya ke aiko sakonnin ingiza tayar da hankali.

“Ba dai dai ba ne a mayar da hankali a kan asara ta yanki guda da ya faru a Legas, alhali ga wadanda ba su ji ba basu gani ba, amma a ka kashe wasu daga cikinsu a ka wawushe dukiyarsu sannan a ka kona wasu,” inji mai magana da yawun kungiyar.