Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin yin tafiye-tafiye tsakanin dukkan jihohin Najeriya.
Gwamnatin ta kuma sanar da amincewar a bude makarantu ga dalibai da ke shirin jarrabawar kammala karatun firamare da sakandare.
Hakan na zuwa ne a ranar Litinin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi rahoto na biyar daga kwamitinsa na kar-ta-kwana kan yaki da cutar coronavirus, kan halin da ake ciki game da cutar a kasar.
- Muhimman abubuwan da su ka faru a makon jiya
- COVID-19 ta kashe mutum a 500,000 duniya
- An haifi ‘yan uku masu dauke da COVID-19
“Ina farin cikin shaida muku cewa Shugaban Kasa… ya amince, sai dai ‘yan sauye-sauyen da za a sanar a nan gaba”. inji Bos Mustapha, shugaban kwamitin.
Sai dai ya ce tafiye-tafiyen za su fara ne daga ranar 1 ga watan Yuli, tsakanin karfe 5 na Asuba zuwa 10 na dare da a baya aka kebance manyan motoci masu dakon kayan abinci da kayan gwari da shi.
Za a bude makarantu
Boss Mustapha ya kara da cewa Shugaba Buhari ya amince a bude makarantu ga daliban ‘yan aji shida na firamare, da kuma ‘yan aji uku na karamar sakandare da kuma ‘yan aji uku na babbar sakandare da ke shirin jarabawar kammala karatu.
Sai dai ya kara da cewa nan gaba za a sanar da matakan da za a bi wajen bude makarantun.