Gwamnatin Jihar Kano, ta fara shirye-shiryen ƙaddamar da kasuwar gwal da aka yi wa laƙabi da (Gold Souk), wacce za ta zama cibiyar tace ɗanyen gwal a Arewacin Najeriya.
Kwamishinan Ma’aikatar Ma’adinai ta jihar, Safiyanu Hamza Kachako ne, ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba aiki ksuwar da ke Batakaye a yankin Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar.
- Jawabin Tinubu ya nuna akwai mafita game da matsalolin Najeriya — Jigon APC
- Muhimman ayyukan ci gaba da gwamnatina ta yi a watanni 14 — Tinubu
Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ne, ya gina kasuwar a shekarar 2021.
A cikin takardar da daraktan wayar da kai na ma’aikatar, Adamu Ibrahim Dabo, ya sanya wa hannu Kwamishinan ya yi alƙawarin ganawa da Ministan Ma’aikatar Ma’adinai don ganin kasuwar ta fara aiki.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙirƙirar ma’aikatar da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi abu ne da ya dace domin zai taimaka wa jihar wajen samun kuɗin shiga tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar za ta yi duk me yiyuwa wajen ganin ta haɗa gwiwa da duk masu ruwa da tsaki a Najeriya da ma ƙasashen ƙetare don ganin haƙarsu ta cimma ruwa.