Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da umarnin sake bude wasu kasuwanni hudu da aka rufe a jihar saboda matsalar tsaro.
A baya gwamnatin jihar ta rufe kasuwannin ne sakamakon rahoton barazanar hare-hare da ’yan bindiga ke iya kai wa kan kasuwannin.
- ’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Zamfara
- Kotun Musulunci ta daure barawon talo-talo wata 2 a Kano
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), ya rawaito cewa a baya-bayan nan Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umarnin bude wasu kasuwanni bakwai da suka hada da Kasuwar Kaura Namoda, Kasuwar Daji, Kasuwar Gusau, Kasuwar Danjiba, Kasuwar Tsafe, Kasuwar Talata Mafara da kuma Kasuwar Gummi.
Kwamishinan Yada Labaran jihar, Ibrahim Dosara, ya sanar ranar Laraba a Gusau cewa nan ba da jimawa ake sa ran bude kasuwannin Dansadau, Maradun, Bungudu da Maru.
“Hukuncin sake bude kasuwannin ya zo ne bayan samun rahoton daidaituwar al’amuran tsaro a yankunan,” a cewarsa.
Kazalika, ya ce gwamnatin jihar ta cim-ma matsaya da shugabannin kasuwannin cewa za su sa ido tare sa dakile faruwar laifuka a kasuwannin.
Sannan ya bayyana godiyar gwamnatin jihar kan yadda jama’ar jihar ke bayar da hadin kai da kumma addu’o’i da suke mata.
Dosara ya jinjina wa jami’an tsaro a jihar kan yadda suke namijin kokari wajen tabbatar da tsaro da kuma yaki da ’yan bindiga.
Ya kara da cewa ana ci gaba da samun kyakkyawan sakamako a yaki da ake yi da ’yan bindiga a jihar.
Dosara, ya tabbatar wa da jama’ar cewa gwamnatin za ta ci gaba da kare rayukansu da dukiyoyinsu.