Hukumomin tsaro da Gwamnatin Jihar Borno sun gudanar da bikin bude hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Bama zuwa garin Banki mai tsawon kilomita 150.
Hanyar, wadda ta hade da kan iyakar kasar nan da Kamaru, garuruwan da suke kanta sun shahara a harkokin kasuwancin dabbobi da kayayyakin bukatun yau da kullum, sai dai ta kwashe sama da shekara hudu a rufe, sakamakon rikicin Boko Haram da ya faro sama da shekara bakwai, al’amarin da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar da na yankin Arewa maso Gabas.
Sakataren kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Borno, Alhaji Amadu Musa, ya shaida wa wakilinmu jin dadinsu kan bude hanyar, ya ce, “A gaskiya mu ’ya’yan kungiyar direbobin motocin sufuri, muna godiya ga Allah da kuma su kansu jami’an tsaro da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno saboda bude wannan hanya, domin tun fara wannan rikici na Boko Haram, jami’an tsaro suka rufe akasarin hanyoyin da suka hade Jihar Borno da sauran jihohi da kuma kasashen makwabta uku,wato Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi, sai wannan hanyar kawai da ta tashi daga Maiduguri zuwa Damaturu zuwa Kano ko zuwa Bauchi zuwa Jos ta saura. Amma sauran wadancan duk a rufe suke saboda matsalar tsaro. Kuma kowacensu ta kwashe sama da shekara uku a rufe.” Ya kara da cewa, “A sakamakon haka harkokin kasuwanci da sufuri sun tsaya cik ga al’ummar Jihar Borno da sauran abokan huldarsu daga sassan kasar nan da kuma wadancan kasashe uku, babu wani ci gaba. To amma Allah cikin ikonSa sai Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya bude mana hanyar Maiduguri zuwa Damboa zuwa garin Biu, sai kuma hanyar Maiduguri zuwa Dikwa zuwa Gamboru-Ngala, ga shi kuma a yau an bude mana hanyar Maiduguri zuwa Bama zuwa garin Banki kuma duk wadannan hanyoyi manya ne, wadanda suka hade kan iyakokin Najeriya da kasashen makwabta.”