✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude bankuna, an sassauta dokar kullen COVID-19

Daga yanzu bankuna a fadin Najeriya za su ci gaba da aiki kamar yadda aka saba kafin bullar cutar COVID-19. Za kuma a bude harkar…

Daga yanzu bankuna a fadin Najeriya za su ci gaba da aiki kamar yadda aka saba kafin bullar cutar COVID-19.

Za kuma a bude harkar sufurin jiragen sama na cikin gida daga ranar 21 ga watan Yuni da muke ciki.

Kazalika Gwamantin Tarayya ta mayar da dokar hana fita a fadin kasar karfe 10 na dare zuwa karfe 4 na asuba.

Shugaban kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 Dr Sani Aliyu ya sanar da haka a lokacin jawabin kwamtin a ranar Litinin.

Ya kuma sanar da bude masallatai da coci-coci bisa wasu ka’idoji na dakile yaduwar cutar coronavirus a bainar jama’a.

Ya ce “Manufar ita ce rage cudanyar mutane domin takaita yaduwar cutar coronavirus.”

Bude makarantu ba yanzu ba.

Sai dai ya bayyana cewa makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe zuwa nan gaba.

Haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi na nan har yanzu, yayin da za a ci gaba takaita cakuduwar mutane a kasuwanni.

Kazalika harmacin taruwar mutane fiye da 20 a wajen wuraren ibada ko wuraren aiki na nan ba a janye ba.

“Za a takaita shigar jama’a kasuwanni da cibiyoyin kasuwanci. “Hukumomin jihohi za su sanar da lokutan bude wadannan wurare,” inji shi.

Jawabin ya kara da cewa wuraren shakatawa da na motsa jiki da gidajen abinci za su ci gaba da zama a rufe sai abin da hali ya yi.

Amma an yi wa gidajen abinci sassaucin sayar da abincin da za a tafi da shi a ci a wani wuri.