Gwamman Jihar Bauchi, Muhammaed Abubakar ya yi wa iyalan marigayi, Alhaji Garba Gadi ta’aziyya a gidansa da ke garin Azare bayan da aka yi jana’izarsa a ranar Asabar din da ta gabata.
Dubban jama’a wadanda suka hada da Gwamna Muhammed Abubakar da Kakakin Majalisar jihar, Kawuwa Shehu Damina da sauran jami’an gwamnati da ’yan siyasa da masu rike da sarautun gargajiya suka halarci jana’izar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Garba Muhammad Gadi.
Marigayi Gadi wanda ya rasu ranar Talatar da ta gaba a kasar Indiya, an binne shi ranar Asabar din da tagabata bayan an yi masa sallar jana’iza bisa dokokin addinin musulunci.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Garin Azare, Malam Ayuba Muhammed shi ne ya jagoranci sallar jana’izar.