An yi jana’izar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, an kuma binne shi da misalin karfe 10:05 na safiyar Lahadi a gidansa da ke Badun, babban birnin jihar.
An dai binne marigayin ne cikin tsauraran matakan tsaro a gidansa da ke rukunin gidaje na Oluyole a maimakon gidansa da ke Agodi GRA wanda tun da farko nan ne iyalansa suka so a binne shi, amma gwamnatin jihar ta ki amincewa bisa dalilan rikicin da ke tattare da mallakar gidan.
Malaman Addinin Musulunci da suka jagoranci jana’izar marigayin sun haɗa da Alhaji Kunle Sanni, da Sheikh Muhyideen Bello, da Babban Limamin garin Badun, Sheikh Abubakri AbdulGaniyu Agbotomoke , da sauransu.
- Kalli yadda masu ta’aziyya suke juyayi a gidan Ajimobi
- Tarihi da rayuwar Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan Oyo
An binne shi ne bisa bin tsarin matakan kare yaduwar Coronavirus.
An kuma shirya masa addu’a ta musamman a masallacinsa da ke Oke-Ado a birnin na Badun.
Marigayi Ishaq Abiola Ajimobi ya rasu yana da shekaru 70 ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni bayan ya yi fama da jinyar COVID-19 da wasu cututtukan da suka taba bangarorin jikinsa.