✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An binne marigayi AVM Mukhtar Muhammad a Kano

An binne gawar Tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, marigayi AVM Mukhtar Muhammad a Kano. Jirgin wani kamfani mai zaman kansa ne ya dauko gawar daga…

An binne gawar Tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, marigayi AVM Mukhtar Muhammad a Kano.
Jirgin wani kamfani mai zaman kansa ne ya dauko gawar daga birnin Landan zuwa filin saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 7 da minti 35 na daren jiya.
Matarsa, Hajiya Rabi Mukhtar Muhammad tare da ’ya’yansa biyu, Abba Mukhtar Muhammad da Mukhtar Muhammad su ne suka rako gawar daga birnin Landan zuwa Kano.